Allahu Akbar; Yarinyar Da Ta Ga Manzon Allah A Fili Ta Gudanar Da Zagayen Maulidi A Zariya.
Allahu Akbar; Yarinyar Da Ta Ga Manzon Allah A Fili Ta Gudanar Da Zagayen Maulidi A Zariya
“An hagi Sayyada Ruƙayyatu bisa doki da tawagarta a ranar zagayen Maulidin Manzon Allah (SAW) a garin Zariya Jihar Kaduna wanda ya gudana a ranar Lahadi.
Yarinyar da kullum ake tururuwa zuwa ganinta domin samun tabarraki daga wurinta mai suna Ruƙayyatu wacce suke kiranta da (Sayyada) haifaffiyar garin Zariya a wani Anguwa da ake kira Kusfa gidan (Ɗan Asama), a cewarta ta ga Manzon Allah (SAW) Ido da ido a cikin sufa mai kyau a zahiri da kuma cikin mafarki.
“Tun bayan faruwar wannan al’amari iyayenta suka killaceta a gida bata zuwa ko’ina, duba da yadda ɗaruruwar Al’ummane a garin Zariya har na wasu garuruwa suke zuwa ziyarar gani da ido wurinta su samu tabarraki.