Wani Babban Soja Ya Kirani Munyi Magana Fiye Da Minti 30 Akan Maganar Seaman Abbas jikina yayi sanyi sosai wlh…
Wani Babban Soja Ya Kirani Munyi Magana Fiye Da Minti 30 Akan Maganar Seaman Abbas jikina yayi sanyi sosai wlh..
Daga Ibrahim Jamila
Magana ta Allah kar ayi using karfi da viol*ence inba hakan ba za’a kara implicating dinsa ne a nemi afuwa kawai a sassauta masa …
A doka abunda yayi zai iya dadewa sosai a garkame ba’aji duriyarsa ba …
Da farko cikin laifinsa da aka bayyana min ba masallaci yaje ba , Brigade MS zaiyi addressing dinsu da safe misalin karfe goma na safe baizo da wuri ba sai Abbas da abokinsa suka fita basu dawo ba sai da aka gama addressing sauran mutanen ..
Da aka hangoshi yana zuwa ogansa yace daga Ina yake bai amsa ba , akace masa you’re stup!d yace he’s not stup!d dey should address him by his name and rank , nan ne ran ogansa ya baci yace ayi disarming dinsa …
Sojoji sunje suyi disarming dinsa yaki yasa taurin Kai yayi cocking bindiga garin a kwace har sai da bindiga ya harba …
A doka idan kayi cocking bindiga wa oganka a soja tamkar kayi niyyar kisa ne kuma laifinka babba ne babu abunda zai fitar da Kai sai anyi maka hukunci mai tsauri …
Laifi dai shi ya jawa kansa , abunda ya kamata ayi a yanzu shine neman alfarma sabida tausayin iyalansa ..
Cikin bayanin da sojan yamun yace ansha aje kotu dashi wajan shara’a sai yasa taurin Kai yayi shiru yaki magana , sau uku Ana zuwa kotu baya bayani shiyasa ma aka barshi a daure ba’a yanke masa hukuncin da ya dace dashi ba …
Wannan rubutun nayi sa bisa abunda sojan yace min ya rage a tsaurara bincike aji gaskiyar lamari a kuma San ta yaya za’a shawo kan lamarin